Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Cibiyar bincike ta duniya ta Waliyyul Asr (A.S) ta dauki shekaru tana aikace-aikace da himma domin yada ilimin mahadiyyanci karkashin jagorancin Ayatul-Lahi sayydi Mahamud Baharul Ulum da kuma karfafawa daga marja'o'i masu girma da daraja da kuma goyon baya da gudummuwar daliban hauzozi da na jami'o'i.

Cibiyoyin da suke da alaka da wannan cibiya suna da ayyuka da suka shafi batun mahadiyyanci da  a takaice su ne:

·        Laburare ta musamman game da mahadiyyanci

·        Sayet din duniya na Ittila' rasaniye imam Mahadi (A.S)

·        Cibiyar binciken addinai da akidoji

·        Cibiyar al'adu da yadawa

·        Yin tarurrukan duniya game da mahadiyyanci

·        Cibiyar binciken karshen zamani

 

Ayyukan cibiya

Yin daurar koyarwa domin sanin mahadiyyanci

Yin taron duniya game da mahadiyyanci kamar haka:

·        Fikirar mai kawo gyara abin alkawarin zuwansa da asalin mahadiyanci

·        Mahadi (A.S) a mahangar addinai da mazhabobi

·        Bincike game samuwar imam Mahadi (A.S)

·        Sanin tawaya da kuma tarbiyyar samari a zamanin boyuwar imam mahadi (A.S)

·        Sauraron imam Mahadi da kuma ayyukan da suka hau kan masu sauraro

·        Duniya na sauraron bayyanar mai gyara abin alkawari

·        Daular bullowar rana da kuma lokacin bayyana mai daraja

·        Duniya, sinima, da karshen zamani

·        Tafarkin masu sauraro da mahadiyyanci

·        Raja'a ko daula mai daraja

·        Bayanin Mai tseratarwa a sarkar intanet

·        Kalmomin bayyana

·        Duniya da mahadiyyanci

·        Kallo zuwa ga tafarkin hukumar imam Mahadi (A.S)

·        Kiristanci da yammacin duniya zuwa ga tarbiyya da mahadiyyanci

·        Al'ada da mahadiyyanci

·        Sanin littattafan da suka yi bayanin Mahadi

Taron ilimi da bincike da halartar mutane daga kasashe daban-daban:

·        Parfessa Liken Howzin Ba'amerike

·        Dr. Tijjani Samawi Batunese

·        Istiwili Kilaude Bafaranshe

·        Dr Isam Imadi Yemen

·        Hasan Shuhata Bamisre

·        Robato Aredi Ba'italiye

·        Dahir Hassan Ba'amerike

·        Robato Raiko Ba'italiye

·        Dr. Ali Linistad Dan Nowey

·        Dr. Ali Kuga Bajamuse

·        Dr. Husain Labiyal Bajamuse

·        Dr. Abdul Khalik Aiman Bamisre

·        Dr. Harish Waldman Dan Austiraliya

·        Amir Abu Darik Batuen Dan Ingila

·        Sailh Al-Wardani Bamisre

·        Yusif Kabisof Barushe

·        Ahamd Hanif Dan Kanada

·        Abdulsalama Al-Lagmish Dan Bulgariya

·        Furijo Lumunuku Ba'italiye

·        Abdul Wahid Barushiye

·        Hasan Shamsuri Dan Malaisiya

·        Ibrhim Zinko Ba'afrike

·        Mika'il Bus Ba'amerike

·        Dr. Ali Alshaikh Ba'irake

·        Abdul Baki Dan Aljeriya

·        Muhammad Nadim Zainal'uf Barushiye

·        Shams Al-Sharif Dan Indunisiya

·        Shaikh Hafiz Muhammad Dan Nijeriya

·        Mrs. Kazrum Fatima Barushiya

·        Mrs. Hasina 'Yar Ingila

·        Mrs Nusrat Bnt Muhammad Isa 'Yar Malaisiya

·        Mrs Zainab Alhisi Bajamusa

·        Da sauransu masu yawa

·        Assasa babbar laburare da ta kunshi bayanai game da imam Mahadi (A.S)

·        Taron Tattaunawar adidinai da mazhabobi da halartar masana kwararru na waje da cikin Iran

·        Kafa sashen intanet na duniya na ittila rasaniye imam Mahadi (A.S) da harsuna masu yawa domin isar da sakon mazhabin Ahlul Bait (A.S) musamman binciken mahadiyyanci da kuma tambaya da amsa da harsuna masu yawa da suka hada:

Larabci, farisanci, ingilishi, faransanci, italiyanci, jamusanci, yaren cana, turkanci, sipeniyanci, inidyancic, bosniyanci, yaren urdu, indunissiyanci, rashanci, bangalanci, harshen hausa, (yarurruka 16 ne) kuma in Allah ya so zai kai yarurruka 40 nan gaba.

Samara da CD da kuma sauran kayan isar da sako game da mahadiyyanci da kuma laccoci na wadanda suka musulunta ko kuma suka zama Shi'a.

Buga littattafai da makaloli da kuma raba su.

Yin daura game da sanin shi'anci da kuma bahasosi na akida da kuma aika masu tabligi zuwa yankuna daban-daban domin isar da sakon da kuma shiryar da su zuwa ga sanin mazhabar Ahlul Bait da imam Mahadi (A.S)

Yin taro na duniya game da imam Mahadi (A.S) a ciki da wajen Iran domin daukaka matsayin ilimi da bincike na samari a kan maudu'o'i masu yawa game da imam Mahadi (A.S) da kuma bahasosin cancantar Shi'anci.

Amfana daga darussan malaman hauza da jami'o'i kamar:

Ayatul-Lahi Sheikh Abdulhusain Khurasani

Ayatul-Lahi Rahamani Hamdani

Ayatul-Lahi Fakih Imami

Ayatullhi Karimi Jahumi

Ayatul-Lahi Muzahiri

Ayatul-Lahi Dibadaba'i

Hujjatul Islami Wal Muslimin Mahadi Pur

Nazri Munfarid

Mu'awiniyan

Ali Dawani

Eskandari

Dabasi

Wasik

Asadi Karamwardi

Dr. Nahawandiyan

Dr. Ansari

Dr. Tamuri

Yin jalasosi na bincike da kuma gudanar datattaunawa game da tabbatar da gaskiyar shi'anci da kuma tunanin da ra'ayoyin sauran malaman addinai game da musulmi da mazhabar Shi'a kamar:

Zuwan injiniya Szu Ruhullahi ma'abocin bincike kuma masanin kompita daga japan

Zuwan maulawi sheikh abudrraham al'Ali adilimi mai huduba kuma limamin jumma'a na garin anar Iraki

Zuwan Injiniya Kerisatl Ali daga siwidin (Sweden)

Zuwan Injiniya Lanart Pitr Ali Suran daga Denmak

Zuwan Malam Doris Kolizn daga zamani

Tattara wajen kusan littattafai 2000 na littattafai a maudu'ai daban-daban game da mahadiyyanci da yaren faransanci, larabci, ingilishi, urdu, tailandanci, indiyanci, rashanci, suwahilanci da …

Assasa cibiyar ginjineye kitab da ta tattara littattafai 35,000 a kan maudu'ai kamar haka: akida, sanin Allah, fikihu, usul, tafsiri, hadisi, tarihi, rijal, falsafa, mandik, kyawawan halaye, addinai da mazhabobi da …

Tattara sama da littattafai da rubuce-rubuce 1000 masu daraja a kan maudu'ai masu yawa.

Yin sama da sididdika 8000 na fila-filai game da maudu'ai musamman da suka shafi samuwar imam Mahadi a duniya domin amfanin mutane.

Yin taron duniya game daimam mahdai daga 10-20 na sha'aban mai grima da karfafawar gwiwa daga marja'o'i da kuma hadin gwiwar cibiyoyin ilimi na mazhabobi da kuma kungiyoyin ilimi da hauzozi da jami'o'i da kuma cibiyoyin duniya da na yada sako da isar da shi game da samar da duniya daya da hada bukukuwan da suka shafi mahadiyyanci a garuruwa da kasashe domin sanin da kuma dada kauna game da imam Mahadi (A.S) da kuma shara fagen yakin al'adu da kuma kare mutane daga karkatar akida da ta kyawawan halaye.

Kafa wata jama'a masu bincike da hadafin yada al'adu game mahadiyyanci da kuma tsara da rubuta mafi girman rubutu game da imam Mahadi (A.S).

Buga littattafai domin raddi ga masu ilhadi da musun samuwar Allah da kuma amsa ga masu sabawa musulunci, da wilaya, da mahadiyyanci, da kuma tabbatar matsayin imam Mahadi (A.S) musamman rayawa da kuma fassara littattafan akida da suka shahara na malami mai girma kuma masanin fikihu babba, malamin masu hikima, da masu sanin Allah, malami na uku, sayyid Muhammad Bakir alhusaini wanda ya shahara da mirdamad ta hannun cibiyar al'adu da buge-buge ta Bahar Kulub.

Samar da sidin fila-filai na imam Mahadi, da kuma teburan tattaunawa, samar da musabakar samari, tambaya da amsa da kuma nuna tashoshin telebijin musamman game da Shi'a a setalayet.

Neman kafa da kuma taimakawa domin samar da cibiyoyi 313 game da imam Mahadi da kuma cibiyoyin ilimi da masallatai da hauzozi, da kuma jami'o'i da husainiyyoyi a ciki da wajen Iran (Turai, Amurka, Kanada, Gabas ta Tsakiya, Asiya ta Tsakiya, Afrika, da Asiya ta gabas) wadanda a wannan al'mari suna da alaka da kusan cibiyoyi 24 kuma muna sanar da sauran cibiyoyi cewa a shirye muke domin samun alaka da su.

Hadafinmu shi ne samun yardar imam Mahadi (A.S) da kuma koyi da littafin Allah da Ahlul Bait da kuma yada musulunci musamman a cikin mazhabar shi'anci ta hanyar riko da ayoyi masu haske na kur'ani da hadisan alayen Annabi (S.A.W).