Home Page | About US | Contact Us |
 

Hikimar Imani Da Mai Tseratarwa

Ba kokwanto cewa duk wani juyi a duniya yana dauke da wata fikira da yake son isarwa da yadawa, amma fikirar juyin imam Mahadi (A.S) zata kasance musulunci ne, wannan fikira zata zama sanadiyyar rushewar zalunci ta hanyar nuna adalci da yanayin walwalar jin dadin al’umma da ake hankoron kaiwa gareshi.

Fikirar Juyin Duniya Na Imam Mahadi

Tun da musuluncin da Mahadi (A.S) zai nuna wa duniya shi ne mafi kosar da bukatun dan Adam, saboda haka ne zai kasance dalilin motsi mai girma domin rushe zalunci da sadaukarwa da yakar azzalumai.

Mafi girman asasin da za a yi kira zuwa gareshi shi ne tsayar da adalci, al’amarin da mafi yawan ruwayoyin Shi'a da Sunna da zuka zo suke nuni zuwa gareshi, kuma ta hanyar fassara kur’ani da tafsiri mai inganci da sahihin tawili wannan zai kai ga rushewar sauran fikirorin da sauran addinai suke dauke da su.

Wannan fikirar ta imam (A.S) tana kunshe da taken cewa: “Da adalci ne sammai da kasa suka tsayu”[1]. Don haka ne samar da adalci ya kasance mafi girman asasin addinin ubangiji kamar yaddda koyarwar kur’ani mai girma ta nuna, aikin annabawa shi ne tsayar da adalci a cikin al’umma da taimakon mutane garesu[2].

Koda yake annabawa da suka gabata sun tsayar da adalci amma bai samu yaduwa ko’ina a sasannin duniya ba, sannan ya bayyana cewa: juyin imam Mahadi (A.S) wani juyi ne na addini da yake a fili.

A wannan juyin ana kore duk wani tunani na rashin imani da addini, kuma addini ba kawai yana takaita da daidaikun mutane ba ne a al’amarinsu na kashin kansu, har ma yana kasancewa wani abu ne na al’umma da zamantakewa da ya shafi al’amarin mutane a rayuwarsu ta al’umma a tare gaba daya

Haka nan juyin imam Mahadi (A.S) wani juyi ne da ba a iya kwatanta shi da wani juyi na dan Adam, kamar juyin Faransa da da na Rasha, da na Cana, kamar yadda ba a iya kwatanta shi da wani juyi ta fuskancin tunani. Misali demokradiyyar jari-hujja an kafa ta a kan daidaito tsakanin mutane wanda ba ta iya samar da komai ba a wannan fage, kuma dalilin asalin rashin cin nasarar ta ya faru ne daga gabar da take yi da addini. Amma juyin imam Mahadi (A.S) ya doru kan asasin addini ne, kuma zai samar da ‘yancin daidaito na hakika da adalci ga kowane mutum.

Kuma a bisa dabi’a addinin duniya wanda bai kebanta da wani bangare ba shi ne zai iya kawo sauyin duniya, wannan addini kuwa a mahangar Shi'a shi ne addinin musulunci wanda yake kunshe da asasosin dukkan addinan ubangiji, kuma gurbata ba ta same shi ba, kuma kalubalen da kur’ani ya yi har yanzu wani addini bai ba shi amsa ba, don haka shi ne addini tsantsa a wajen Allah: “Hakika addini a wajan Allah shi ne musulunci” (Ali imran: 19).

Da fadinsa: Duk wanda ya nemi wani addini ba musulunci ba, ba za a taba karba daga gareshi ba (Ali imran: 85).

Da fadinsa: Allah yana umarni da adalici da ihsani (Nahal: 90).

Da fadinsa: Idan kun fada to ku yi adalci (An’am: 152).

Da fadinsa: ku yi adalci shi ne ya fi kusa da takawa (Ma’ida: 8).

Da fadinsa: Hakika mun aiko manzannnimu da hujjoji kuma muka saukar da littafin da ma’auni tare da su domin mutane su tsayu da adalci (hadid: 25)

Wani muhimmin abu kuwa shi ne a mahangar musulunci; duk inda mutane suke rayuwa a kowane yanki ne na duniya, da kowane irin yare ne suke magana, da kowace al’umma ce da kalar ko launin fatarta, dukkansu dangi daya ne, kuma sun zo daga asali daya na uwa da uba daya, kuma a girmamawar mutumtakarsu duka daya ne[3]. Don haka ne maganar kallafa musu aiki ta fuskantarsu bisa daidaito, da cewa: “Ya ku mutane”, ko kuma “Ya ‘yan Adam”. Kur’ani ya yi kakkausan suka game da kabilanci, da bambancin launin fata:

“Ya ku mutane mu mun hallice ku daga maza da mata, muka sanya ku jama’u da kabilu domin ku san juna, hakika mafi girmanku a wajen Allah shi ne mafi takawarku” (Hujurat: 13).

Hadisin Manzon Allah a hajjin bankwana yana cewa: “Ya ku mutane ku sani ubangijinku daya ne, kuma hakika babanku daya ne, ku saurara ku ji, babu fifiko ga balarabe a kan ajami, ko ajami a kan balarabe, ko ja a kan baki, ko baki a kan ja sai dai da takawa”[4].

Don haka a bisa wannan mahanga zamu samu cewa musulunci shi ne addinin daidaito, da adalci da karama a fadin duniya, fadin Manzon Allah (S.A.W):

“Shin ba na ba ku labarin Mahadi ba, da za a tashe shi a cikin al’ummata a lokacin sabanin mutane da kaskanci, sai ya cika duniya da adalci da daidaito bayan an cikata da zalunci da danniya, mazauna sama da mazauna kasa zasu yarda da shi, yana raba dukiya da yawa bisa daidaito. Sai wani mutum ya ce: menene daidaito? Sai ya ce: Daidaita wa tsakanin mutane, zai kuma cike zukantan mutane da wadata, ya yalwace su da adalcinsa[5]”.

Ana iya cewa musulunci duk da ya kasance wani abu ne dadadde amma kuma zai kasance sabo, duba fadin imam Sadik (A.S): Daga Abu basir daga Abu Abdullah (A.S) ya ce: …kamar ina ganin sa a tsakanin rukuni da Makamu Ibrahim yana karbar bai’ar mutane a kan sabon littafin da al’amarinsa mai tsanani ne a kan larabawa[6].

Imam Bakir (A.S) yana cewa: Na rantse da Allah kamar ina gannin sa tsakanin rukuni da makamu Ibrahim yana karbar bai’ar mutane a kan sabon al’amari da sabon littafin, da sabon iko daga sama[7].

Idan mun duba zamu ga abubuwa biyar da wadannan ruwayoyi da wasunsu suka kunsa su ne:

Al’amari sabo

Sunna sabuwa

Hukunci sabo

Karfin iko sabo

Kira sabo

Amma batun cewa ya zo da addini sabo kamar yadda ya zo daga maganganun wasu mutane ba shi da inganci[8].

Haka nan tunanin cewa zai zo da wani kur’ani daban ba wannan ba wannan ma batacce ne, domin Mahadi mai imani ne da littafin Manzo da sunnarsa, kuma babu wata mazhaba da take da kokwanto a kan hakan[9]. Imam Ali yana cewa: Sai ya nuna muku yanda hanyar adalci take, ya raya matacce daga Kur’ani da Sunna[10].

Ba komai raya matacce yake nufi ba sai gyara tafsirin barna da karkata da ake yi wa littafin Allah da fitar da ma’ana da tawilinsa na gaskiya, da fitar da badininsa na ainihi, kuma wannan yana nufin hukumar Allah a bayan kasa da gudanar da adalci a dukkan duniya.[1] Safinatul bahar, j 2, shafi: 166.
[2] Hadid: 25.
[3] Imamat wa mahdawiyyat, j 2, shafi: 69.
[4] Abin da ya gabata.
[5] Muntakhabul asar, b 1, f 2, shafi: 147, h 14.
[6] Al’gaiba, Nu’umani, shafi 102.
[7] Abin da ya gabata, shafi: 139.
[8] Tarihu ma ba’adaz zuhur, shafi: 637 – 639.
[9] Abin da ya gabata: 649 – 655.
[10] Nahajul balaga, huduba: 138 – 425.