Home Page | About US | Contact Us |
 

Alamomin bayyanar imam Mahadi (A.S)

Ta yiwu muna iya cewa al’amarin bayyanar imam Mahadi (A.S) a mahangar Shi'a wani abu ne da Allah ya boye shi kuma ya zama sirri domin samun nasarar imam Mahadi (A.S) a kan makiyansa, don haka ne ma ruwayoyi suka zo suna karyata duk wani wanda yake ayyana lokaci; kamar wata ko shekara ko ranar da zai bayyana.

Amma za a iya bayanin alamomin bayyanarsa a dunkule kamar bayyanarsa a ranar ashura ko kwankin da suke wutiri ba shafa’I ba kamar ranar asabar. Sai dai ba yadda za a iya sanin wace ashura ce zai bayyana ko wace asabar ce ko jumma’a. Koda yake ruwayoyin da suka nuna shekarar bayyanarsa a wutiri take ‘yan kadan ne, amma cewa ranar ashura zai bayyana wannan ya zo da ruwayoyi masu yawan gaske da za a iya tabbatar da shi[1].

Ta kowane hali dai ba wanda ya san lokacin bayyanara sai Allah, kuma duk sadda ubangiji ya so ya bayyanar da shi to wannan zai tabbata, sai dai a dunkule idan mun duba ruwayoyi da hadisai zamu ga wannan bayyanar a kusa take idan an samu:

1- Fadawar mutane daidaiku da al’umma gaba daya cikin halin yanke kauna.

2- Gazawar addinan daga samar da abin da suke da’awarsa, kamar tsarin jari-hujja da ya gaza samar da ‘yanci na hakika, da kuma kwaminisanci da ya kasa samar da adalcin zamantakewa da na tattalin arziki da sauransu.

3- Wulakanta kimar addinan Allah a cikin al’ummu kamar bayyanar da munkarai da munanan dabi’u da halaye, kuma da halatta su kamar neman jinsin juna kamar dabbobi, da cin riba, da cin dukiyar mutane, da halatta giya da sauran kayan maye, da yawaitar saki, da karo da juna tsakanin aiki da zance, da cin shubuha, da yawaitar zina da zubar da jini, da halatta yin karya, da cin rashawa, da yanke zumunci, da yaduwar kage da karya, da bidi’o’I, da shugabancin jahilan mutane, da halatta waka da wasanni da muzik.

Da wulakanta mumini, da fakiri, da malami, da girmama fasiki, da azzalumi, da bata hukunce-hukuncen Allah, da halatta dukkan haram din Allah, da take wajiban Allah a kasa[2].

4- Addini da ma’abotansa zasu zamanto baki a cikin al’ummu, kuma kamar yadda mutane a farkon musulunci suka rika shiga cikin addinin jama’a-jama’a (surar Nasr) haka nan zasu rika fita daga cikinsa jama’a-jama’a[3].

5- Faruwar wasu abubuwa na sama da na kasa da suka hada da[4]:

- Yin ruwan sama na kwana arba’in

- Faruwar fitina da yaki mai tsanani da kashe sama da mutane miliyan uku, da rushe wasu birane da wasu garuruwa da dimuwa da firgici.

- Yaki da kashe-kashe a Iraki da Bagadad, kuma da mamaye ta, kuma da abubuwa masu yawa da zasu faru a Iraki da Kufa da Basara da Bagadad.

- Yunwa da Fari.

- Zuwan tuta tamanin zuwa yakin larabawa. (Ta yiwu tana nufin kasashe tamanin ne).

- Kashe wasu daga sarakuna.

- Motsin wasu mutane da gwagwarmayar neman hakki kamar Yamani, da Sayyid Khurasani, da Hashimi daga Gilana.

- Yaduwar wasu cututtuka masu kisa kamar annoba.

- Faruwar wasu canje-canje a sama kamar sama ta yi ja ta takure, da alamomi a rana da wata kamar bayyanar fuskar Annabi Isa (A.S) a rana da kuma faruwar iska ja da baka.

- Yaduwar wuta a wasu kasashe (tayiwu yaki ne a kan mai)

- Lalacewar ‘ya’yan itace a kan bishiyoyi (tayiwu saboda lalacewar yanayi da waje ne)

- Bayyanar masu da’awar annabta (masu da’awa 60)

- Juyin juya halin masu rauni a kan masu girman kai.

- Bayyanar Dujal.

6- Faruwar abubuwa 5 wadanda faruwarsu dole ne a cikin wasu watanni[5]:

- Bayyanar Sufyani.

- Kisfewa da ruftawar kasa.

- Kashe Nafsuz zakiyya.

- Kira daga sama cewa Mahadi (A.S) zai bayyana da kuma neman yi masa bai’a.

- Bayyanar Yamani

7- Shugabancin tattaunawar azzaluman kasashe kafin bayyanar Mahadi (A.S) wanda zai sanya yaduwar zalunci a duniya ta yadda za a kirga samuwar adalci wani abu ne wanda ba zai yiwu ba.

8- Yankewar kauna daga mutane daga samun gyara da kaunar samun wani mutum daga wajen Allah wanda zai zo domin tseratar da mutane, koda yake wannan al’amari yana bukatar gyara daga su kansu mutane domn Allah ba ya canza wa mutane abin da yake garesu har sai sun canza abin da yake ga kawukansu. (Ra’ad: 11)

Faruwar wannan canjin daga kawukan mutane da kuma taimakon Allah shi ne zai iya bayar da damar bayyanar Mahadi (A.S). Don haka ne neman bayyanarsa daga wajen Allah a aikace da mutane zasu yi yana daga cikin abin da zai sanya hakan, ba kawai a lafazin (maganar) baka ba.

9- Faruwar neman tattauna domin samar da adalci a duniya baki daya. Wannan kuwa zai kasance ne alhalin tattaunawa bisa yin zalunci ta riga ta yadu a duniya kuma ta mamaye ta, sai tattaunawa a kan yin adalci ta zo domin maye gurbin hakan wanda yake yana da alaka da bayyanar imam Mahadi (A.S).

10- Samuwar mutane masu tsarkin zuciya da sadaukarwa domin samar da gudanar da adalci, wadanda suka ci jarabawar Allah da daukaka, kuma suna shirye da yaki a cikin rundunar jagoran karshe.

Da izinin Allah bayyanarsa zata kasance, kuma zamanin juyi da cin nasarar adalci zai zo.

Alamomin bayyanarsa a Injila sun yi kama da wadanda suka zo a ruwayoyin musulmi da zamu yi nuni da su a fasaloli masu zuwa. A Injila bayyanar annabi Isa (A.S) tana tare da dawowar wasu matattu, da kira mai tsawa daga sama, zuwan Isa a kan gajimare da makamantasu[6].

Bayyanar mai tseratar da duniya ya samu tafsiri iri-iri daga mazhabobin kiristoci, AyatulLahi Kashani a tafiye-tafiyensa ya yi tattaunawa da malaman kiristoci yana cewa: “Dukkan mazhabobin kiristoci da ya hada da Katolika, da Protastan, da Okszodokgs, sun yi imani da cewa Masihu (A.S) zai zo. Sai dai na su imanin bai kai na Katolika ba, dukkaninsu sun yarda da daular duniya. Amma zamu iya kasa kiristanci ta fuskanci tunani zuwa kashi uku; bangare na farko masu ganin cewa mas’alar al’amarin bayyanar annabi Isa (A.S) ya shafi Tashin kiyama ne, wato ba su yarda da daular karshen zamani ta duniya gaba daya ba, suna cewa ranar da adalcin Allah zai bayyana ita ce ranar lahira wacce annabi Isa (A.S) ne zai zama mai gudanar da adalcin Allah inda za a bayar da lada ko yin ukuba ga kowa. Wasu kuwa daga cikinsu suna cewa ne: A duniya ne wannan hukumar adalcin zata kafu ta tsayu. Wasu kuwa suna cewa ne: Adalcin ne zai kafu ba hukuma ba[7].

Daga karshe muna cewa: Musulunci ya zo da labarin bayyanar annabi Isa (A.S), wato duniya tana sauraron mutane biyu ne: Na farko Mahadi (A.S), na biyu Isa (A.S) wanda yake waziri ga Mahadi Muhammad dan Hasan Askari (A.S) wanda Isa (A.S) zai yi koyi da shi[8].[1] Sayyid Muhammad Sadar, Tarihi Ma Ba’adaz Zuhur, Shafi: 287 – 296.
[2] Kamil Sulaiman, Ruzegare Rahayi, j 2, Shafi: 701-723. Da Ayatul-Lahi Ludful-Lah Safi Gulfaigani, Muntakhabul Asar, Shafi: 424 – 438.
[3] Littafin da ya gabata, j 2, shafi: 721, hadisi 1721, 1033. Da Muntakhabul Asar, Shafi: 424 – 438.
[4] Littattfan da suka gabata da wasunsu masu yawa.
[5] Abin da ya gabata.
[6] Ruzegarehoye rahayi, Kamil Sulaiman, tarjamar Ali Akbar Mahdifur, shafi: 557 – 568.
[7] - Fasl nameh musahibe bo AyatulLahi Kashani, shekara 2, sh 5, shafi 37 - 56
[8] - Ayatul-Lahi Kashani, mahdawiyyat, kaset na 56, shafi 2, 3, na masallicin Jamkaran.